La Liga za ta binciki sayen Neymar zuwa Barca

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A shekarar 2013 Neymar ya koma Barca daga Santos

Hukumar gasar La Liga za ta bincikiyadda aka yi cinikin Neymar zuwa Barcelona a shekarar 2013.

Mahukuntan na son tattaunawa da Barcelona kan yarjejeniyar da suka cimma wajen sayen dan kwallon Brazil daga Santos.

A watan Yuni Barcelona ta biya tarar sama da fam miliyan hudu wajen sayen dan kwallon mai shekara 24, bayan da aka zargeta da kokarin kaucewa biyan haraji, zargin da ta karyata.

Barcelona ta ce ta sayi dan wasan kan kudi Yuro miliyan 57, inda aka bai wa iyayensa Yuro miliyan 40, Santos kuwa ta karbi Yuro miliyan 17.

Sai dai kuma masu shigar da kara na Spaniya sun ce cinikin ya kai Yuro miliyan 83, kuma Barcelona ce ta yi rufa-rufa. Kungiyar ta karyata aikata ba daidai ba.