Feyenoord ta ci Manchester United 1-0

Gasa Nasara Rashi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

United ta fara wasan farko a gasar Europa da rashin nasara

Manchester United ta yi rashin nasara da ci daya mai ban haushi a hannun Feyenoord a gasar Europa da ta kara a ranar Alhamis a Netherlands.

Feyenoord ta ci United ne ta hannun Tonny Vilhena bayan da ya samu kwallo ta hannun Nicolai Jorgensen.

Jose Mourinho ya saka sabbin 'yan wasa takwas a fafatawa da Fayenoord daga cikin wadanda suka buga karawar da Manchester City ta ci United a gasar Premier.

Kyaftin din United, Wayne Rooney bai buga karawar ba, sai dai an fara wasa da matashin dan kwallo Marcus Rasford.

United tana rukunin farko da ya kunshi Fenerbahce da Zorya Lugansk da kuma Feyenoord Rotterdam.