Bale da Ronaldo ba za su buga karawa da Espanyol ba

La Liga

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Madrid ce ta biyu da maki tara a kan teburin La Liga

Gareth Bale da Cristiano Ronaldo ba za su buga wa Real Madrid wasan La Liga da za ta kara da Espanyol a ranar Lahadi ba.

Bale ya yi rauni ne a wasan cin kofin zakarun Turai da Real Madrid ta ci Sporting Lisborn 2-1 a ranar Laraba.

Shi kuwa dan wasan tawagar Portugal, Ronaldo, ba zai buga karawar ba sakamakon 'yar mashasshara da yake fama da ita.

Real Madrid na fatan yin kan-kan-kan da Barcelona a tarihin lashe wasannin La Liga 16 a jere da ta kafa a 2010/11, idan har ta doke Espanyol a ranar Lahadi.