Man City ta ci gaba da jan ragamar Premier

Man City, sterling

Asalin hoton, Rex Features

Bayanan hoto,

A bana Raheem Sterling ya ci wa Man City kwallo uku

Manchester City ta ci gaba da jan ragamar gasar Premier bayan da ta lallasa Bournemouth 4-0, a wasan mako na biyar a Etihad

Minti 15 da fara wasa De Bruyne ya ci kwallon farko sai Iheanacho ya kara ta biyu a minti na 25.

Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci Raheem Sterling ya zura ta uku ana minti 48 da wasa.

Gündogan ya ci ta hudu kuma ta karshe a minti na 66.

Man City ta rasa dan wasanta Nolito bayan da alkalin wasa ya kore shi a minti 86 saboda ya yi kokarin yi wa Adam Smith na bakin karo.

Da wannan sakamako Man City ta ci gaba da zama jagora a gasar da maki 15, sai Everton mai maki 13, yayin da Arsenal ta zama ta uku da maki 10.

Chelsea ta yo kasa daga ta uku zuwa ta hudu da maki 10, yayin da Liverpool wadda ranar Juma'a ta zama ta hudu yanzu ta dawo ta biyar, da maki 10 ita ma.

Arsenal ta fi Chelsea da bambancin kwallo daya, yayin da ita ma Chelsean ta wuce Liverpool da kwallo daya.