Watford ta casa Man United da ci 3-1

Mako

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Watford ta ci Manchester United 3-1 a wasan mako na biyar

Manchester United tasha kashi a gidan Watford da ci 3-1 a gasar Premier wasan mako na biyar da suka kara a ranar Lahadi.

Watford ce ta fara cin kwallo ta hannun Etienne Capoue saura minti 11 a je hutun rabin lokaci.

Bayan da aka dawo ne daga hutun United ta farke ta hannun matashin dan wasanta Marcus Rashford.

Saura minti takwas a tashi daga karawar Watford ta kara kwallo na biyu ta hannun Juan Zuniga sannan kyaftin din kungiyar Troy Deeney ya ci ta uku a bugun fenariti.

United ta yi rashin nasara a wasanni uku a jere kenan, bayan da City ta doke ta 2-1 a gasar Premier da wanda Feyenoord ta samu nasara da ci 1-0 a gasar kofin zakarun Turai.