Ebola da Shamsu sun buga canjaras a dambe

Dambe
Bayanan hoto,

Shamsu Kanin Emi da Ebola sun buga dambe a Abuja babu kisa

Shamsu kanin Emi da Ebola sun tashi wasan damben gargajiya babu ci a fafatawar da suka yi a gidan dambe na Ali Zuma da ke Dei-Dei a Abuja Nigeria.

Ebola dan damben Kudu da Shamsu daga Arewa sai da suka yi turmi uku babu wanda ya je kasa, daga nan ne Tirabula ya raba karawar.

Gumurzu da aka yi tsakanin Dogon Bunza daga Arewa da Shagon Aleka daga Kudu, turmi uku suka yi, amma babu wanda ya dafa kasa aka raba su.

Damben Nura Dogon Sani daga Arewa da Bahagon Sani Mai Maciji ma turmi uku suka yi babu kisa, haka ma karawa tsakanin Audu Autan Fillo daga Arewa da Bahagon Sisko daga Kudu canjaras suka yi.

Sai dai kuma Shagon Autan Faya daga Kudu ya buge Shagon Shagon Alhazai daga Arewa a Turmin farko.

Shi kuwa Shagon Lawwalin Gusau daga Arewa buge Shagon Shagon Dan Sharif daga Kudu ya yi.

Wasan karshe da aka rufe filin tsakanin Autan Faya daga Kudu da Bahagon Abba daga Arewa tashi suka yi babu wanda ya samu nasara a turmi biyun da suka dambata.