Messi ne kadai ya dara De Bruyne — Guardiola

Mataki

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Manchester City ce ke mataki na daya a kan teburin Premier

Kociyan Manchester City, Pep Guardiola, ya ce Lionel Messi ne kadai ya fi Kevin de Bruyne iya taka leda a dukkan 'yan wasan da ya horar.

De Bruyne, dan wasan tawagar Belgium, shi ne ya fara cin kwallo a karawar da City ta doke Bournemouth 4-0 a gasar Premier da suka yi a ranar Asabar a Ettihad.

Dan kwallon ya buga wa City wasanni 48, ya kuma ci kwallaye 18 sannan ya bayar da kwallon da aka zura a raga har sau 16 a dukkan fafatawar da ya yi wa kungiyar.

Guardiola ya ce idan aka ajiye kujera Messi ne kadai zai zauna a kanta, ba za a amince wani ya hau ba, amma Kevin zai iya dasa tasa a kusa da ta Messi.

Guardiola, wanda ya jagoranci Barcelona da Bayern Munich, ya horar da fitattun 'yan wasan da suka hada da Xavi, da Andres Iniesta, da Arjen Robben, da kuma Thomas Muller.