Nigeria ce ta daya a Afirka a gasar Paralympics

Nigeria

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Nigeria ta taka rawar gani fiye da wadda ta yi a landan a 2012

An kammala wasannin Paralympics na nakasassu da aka yi gumurzun kwanaki 11 a birnin Rio na Brazil.

China ce ta yi ta daya a yawan lashe lambobin yabo, wadda ta ci 238, zinare 106 da azurfa 81 da kuma tagulla 51.

Nigeria ce ta jagoranci Afirka da lambobin yabo 12, zinare takwas da azurfa biyu da tagulla biyu, kuma ta 16 a gasar.

A gasar da aka yi a Landan a 2012 Nigeria ta kammala a mataki na 22, inda ta ci lambobin yabo guda 13, zinare shida da azurfa biyar da kuma tagulla biyu, ta kuma kare a matsayi na uku a Afirka biye da Tunisia da Afirka ta Kudu.

A karon farko Uganda ta ci azurfa a wasa daya da ta shiga a wasannin bana, ita ma Cape Verde ta ci lambar yabo ta tagulla a karon farko a tarihi.

Ga jerin 10 farko na kasashen Afirka da suka taka rawa a Paralympics a Brazil:

  • 1.Nigeria 8 zinare 2 azurfa 2 tagulla = 12
  • 2.Tunisia 7 zinare 6 azurfa 6 tagulla = 19
  • 3.South Africa 7 zinare 6 azurfa 4 tagulla = 17
  • 4.Algeria 4 zinare 5 azurfa 7 tagulla = 16
  • 5.Egypt 3 zinare 5 azurfa 4 tagulla = 12
  • 6.Morocco 3 zinare 2 azurfa 2 tagulla = 7
  • 7.Kenya 3 zinare 1 azurfa 2 tagulla = 6
  • 8.Namibia 1 zinare 2 azurfa 2 tagulla = 5
  • 9.Ivory Coast da Habasha da kuma Uganda 1 azurfa
  • 10.Cape Verde 1 tagulla