Wikki Tourists ta ci Rivers United 1-0

Firimiya

Asalin hoton, LMCNPFL

Bayanan hoto,

Saura wasanni biyu a kammala gasar Firimiya Nigeria

Wikki Tourists ta garin Bauchi ta doke Rivers United da ci daya mai ban haushi a gasar Firimiyar Nigeria wasan mako na 36 da suka kara a ranar Lahadi.

Wikki ta ci kwallon ne ta hannun Waziri saura minti 10 a tashi daga fafatawar.

Da wannan sakamakon Wikki ta koma mataki na uku da maki 54, yayin da Rivers ta fado zuwa matsayi na biyu da maki 56.

Ga sauran sakamakon wasannin mako na 36 da aka buga a ranar Lahadi.

  • Plateau Utd 1-0 Ikorodu Utd
  • Warri Wolves 1-0 3SC
  • Abia Warriors 2-1 Nasarawa United
  • Lobi Stars 2-1 FC Ifeanyiubah
  • Enyimba 0-0 MFM
  • Rangers 2-0 Sunshine Stars