An raba jadawalin cin kofin Afirka a kwallon mata

Asalin hoton, Google
Kamaru ce za ta karbi bakuncin gasar cin kofin Afirka karo na 10 a kwallon kafa ta mata
Hukumar kwallon kafa ta Afirka, Caf, ta raba jadawalin wasan cin kofin nahiyar Afirka a kwallon kafa ta mata.
Gasar da za a yi karo na 10, ta kunshi kasashe takwas a jadawalin da aka fitar a ranar Lahadi a Yaounde, Kamaru.
Rukunin farko ya kunshi mai masaukin baki Kamaru da Masar da Afirka ta Kudu da kuma Zimbabwe.
Nigeria da Mali da Ghana da kenya suna rukuni na biyu.