Za a fara gasar damben mota a jihar Kano

Motar da za a ci a gasar damben gargajiya ta jihar Kano
An raba jadawalin fara gasar damben gargajiya, domin lashe mota ga wanda ya zama zakara a jihar Kano.
Gasar wadda aka yi wa lakani da sunan Mohammadu Sunusi na biyu sarkin Kano, ta kunshi 'yan dambe 32 da za suyi gumurzu a tsakaninsu, domin fitar da gwani.
Za a fara gasar a ranar Litinin da yammaci a gidan wasanni na Ado Bayero Square da ke jihar Kano.
Ga duk wanda ya yi nasara zai lashe mota, na biyu ya karbi babur na hawa da kudi da za a bai wa wanda ya yi na uku da na hudu.
Haka kuma za a bai wa zakaran bana sandar girma ta karramawa saboda bajintar da ya yi.