Dele zai ci gaba da taka-leda a Tottenham

Asalin hoton, Getty Images
Dele ya koma Tottenham da taka-leda daga MK Dons
Dan kwallon tawagar Ingila, Dele Alli, ya sabunta yarjejeniyar ci gaba da murza-leda a Tottenham zuwa 2022.
Alli mai shekara 20, wanda ya koma Tottenham daga MK Dons a Fabrairun 2015 kan kudi fam miliyan biyar, ya tsawaita zamansa zuwa shekara biyar.
Ya fara buga wa Tottenham tamaula a gasar Premier bara, ya kuma ci kwallaye 10 a wasanni 46 da ya yi mata wasanni.
A makon da ya wuce ma Eric Dier, dan kwallon tawagar Ingila, shi ma ya saka hannu kan ci gaba da zama a Tottenham zuwa shekara biyar.