Chelsea za ta ziyarci Leicester a Capital One Cup

Asalin hoton, Getty Images
Chelsea ta lashe Capital One Cup sau biyar a tarihi
Leicester City za ta karbi bakuncin Chelsea a gasar Capital One Cup ta bana a ranar Talata.
Kungiyoyin biyu sun kara a wasan Premier a bara, inda suka yi kunnen doki 1-1 a gidan Chelsea, Leicester kuwa 2-1 ta ci Chelsea.
Chelsea ta lashe kofin Capital One Cup sau biyar a shekarar 1965 da 1997/1998 da 2004/2005 da 2006/2007 da kuma 2014/2015.
Sauran wasannin da za a buga:
- Nottingham Forest vs Arsenal
- Leeds United vs Blackburn
- Bournemouth vs Preston
- Everton vs Norwich
- Derby vs Liverpool
- Brighton vs Reading
- Newcastle United vs Wolverhampton