An ci tarar kociyan Stoke City fam 8,000

Stoke

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Stoke ce ta karshe a kan teburin

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta ci tarar Mark Huges, fam 8,000, bayan da aka kori kociyan a wasan da Tottenham ta ci Stoke City a gasar Premier.

Hukumar ta ci tarar kocin kan nuna halin rashin da'a a karawar da Tottenham ta ci Stoke City City 4-0 har gida.

A lokacin da hukumar ta tahumi Hughes ya ce ba zai daukaka kara ba domin zai yi asarar kudinsa, wanda gwara ya bai wa jikokinsa su kashe.

Kociyan mai shekara 52, ya ce tuhumar da hukumar ta yi masa tamkar kara dagula lissafi ne.

Stoke City tana mataki na 20 a kan teburin Premier da maki daya kacal.