Buhari ya jinjinawa 'yan Paralympic din kasar

Zinare
Bayanan hoto,

Nigeria ta ci zinare takwas da azurfa biyu da tagulla biyu a Brazil

Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya yabawa 'yan wasan Paralympic din kasar kan rawar da suka taka a gasar da aka kammala a birnin Rio na Brazil.

A sanarwar da gwamnati ta fitar a ranar Litinin, shugaba Buhari ya ce masoya wasanni sun jinjinawa 'yan Nigeria na kara martaba kasar da suka yi a Brazil.

Buhari ya kuma yaba da yadda 'yan wasan suka ci lambobin yabo 12, da kafa tarihi a wasan jifan dalma, da yadda suka yi na daya a Afirka a cin lambobin yabo a wasannin da aka kammala a ranar Lahadi.

Haka kuma shugaban ya jinjinawa mahukunta da wadanda suka horar da 'yan wasan da duk wadan da suka bayar da gudummawar wajen daga martabar kasar.