Dan Ali ya buge Shagon Tuwo a damben gasa

Dambe
Bayanan hoto,

Motar da za a lashe a gasar damben gargajiya ta jihar Kano

Dan Ali ya dambace Shagon Tuwo gasar damben mota da aka fara a ranar Litinin a filin wasa na Ado Bayero Square da ke jihar Kano.

A sakamakon gasar wadda aka fafata a wasanni shida, Shagon Dan Bature na kulkul ya buge Dunan ba ta jemu ba a

Shi kuwa Shagon Audu Tunga doke Dan Sama'ila ya yi, Kada Mutsa ya fitar da Shagon Balantina daga gasar.

Shi kuwa Shagon 'Yan Sanda buge Shagon Gwagwarwa ya yi, da karawar da Shagon Shagon dan Digiri ya doke Shagon Sawun Kura.

Gasar wadda aka saka mata sunan Muhammadu Sunusi na biyu sarkin kano za a bai wa zakara mota da sandar girma.