Rangers ta dakatar da Barton

Rangers

Asalin hoton, SNS Group

Bayanan hoto,

Rangers ta ce da Barton ba za su sake yin jawabi ba dangane da danbarwar.

Rangers ta dakatar da Joey Barton mako uku, kwanaki shida tsakani bayan da aka ce ya koma gida lokacin da ya yi sa in sa da abokin kwallonsa.

Barton mai shekara 34, an tuhumeshi da fadawa abokin buga tamaula Andy Halliday da fada masa munanan kalamai.

A jawabin da Rangers da kociyan kungiyar Mark Warburton suka fitar sun ce dukkan 'yan wasan biyu suna bukatar lokaci domin kamo bakin zare.

Kungiyar ta ce da ita da Barton ba za su sake yin jawabi ba dangane da danbarwar.