Sai Toure ya nemi afuwa kafin ya dawo buga wasanni — Guardiola

Manchester

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Manchester City ce ke mataki na daya a kan teburin Premier

Pep Guardiola ya ce sai Yaya Toure ya nemi afuwar Manchester City da abokan kwallonsa kan jawabin da wakilinsa ya yi kafin a dawo saka shi a wasanni.

Toure mai shekara 33, ya buga wa City wasa daya a bana, sannan baya cikin 'yan kwallon da za su yi wa kungiyar wasanni a gasar cin kofin zakarun Turai.

Wakilin Toure a tamaula, Dimitri Seluk, ya ce an ci mutuncin dan kwallon, kuma ya kamata Guardiola ya nemi afuwarsa idan City ba ta lashe kofi ba.

Guardiola ya ce sai Yaya Toure ya nemi afuwa kafin ya dawo buga wa kungiyar tamaula, idan bai yi ba, zai ci gaba da zamansa.