Real Madrid za ta karbi bakuncin Villareal

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid ce ta daya a kan teburin La Liga
Villareal za ta ziyarci Real Madrid a gasar La Liga wasan mako na biyar da za su kara a ranar Laraba.
Madrid tana mataki na daya a kan teburin gasar da makin 12, yayin da Villareal ke matsayi na shida da maki takwas.
A ranar Lahadi Real Madrid ta yi kan-kan-kan da Barcelona a yawan lashe wasannin La Liga 16 a jere, bayan da ta ci Espanyol 2-0.
Sauran wasannin mako na biyar a gasar ta La Liga da za a yi a ranar Laraba, Barcelona za ta karbi bakuncin Atletico Madrid a Camp Nou.
Barcelona tana mataki na biyu da maki tara, ita kuwa Atletico maki takwas ne da ita tana matsayi na hudu a kan teburin La Liga.
- Celta de Vigo da Sporting Gijon
- Real Sociedad da Las Palmas
- Granada da Athletic de Bilbao