Man United za ta ziyarci Northampton

Premier
Bayanan hoto,

United tana mataki na bakwai a kan teburin Premier da maki tara

Northampton Town za ta karbi bakuncin Manchester United a gasar Capital One Cup da za su kara a ranar Laraba.

Manchester United wadda ta yi rashin nasara a wasanni uku a jere ta lashe kofin Capital One Cup sau hudu.

United ta yi rashin nasara a hannun Manchester City da ci 2-1 a gasar Premier da 1-0 da Fayenoord ta doke ta a gasar cin kofin zakarun Turai da 3-1 da Watford ta ci ta a gasar Premier.

Ga sauran wasannin Capital One Cup da za a buga:

  • Swansea City da Manchester City
  • Fulham da Bristol City
  • West Ham United da Accrington
  • Southampton da Crystal Palace
  • Queens Park Rangers da Sunderland
  • Tottenham Hotspur da Gillingham
  • Stoke City da Hull City