Kasashen da za su buga kwallon rairayi a Nigeria

Madagascar

Asalin hoton, The NFF

Bayanan hoto,

Madagascar ce ta lashe kofin farko na kwallon rairayi na nahiyar Afirka

Madagascar ce kasa ta karshe da ta samu tikitin shiga gasar kwallon rairayi ta Afirka karo na biyu da Nigeria za ta karbi bakunci.

Madagascar wadda ta lashe kofin gasar farko ta samu nasara ne a kan Mozambique.

Sauran kasashen da za su fafata sun hada da Senegal da Ghana da Cote D'Ivoire da Masar da Libya da Morocco da Nigeria mai masaukin baki.

Za a fara gasar daga ranar 13 zuwa 18 ga watan Disambar 2016.