Harry Kane zai yi jinya

Asalin hoton, PA
Kane sai cire shi aka yi daga wasan da suka yi da Sunderland a gadon daukar marasa lafiya
Kociyan Tottenham, Mauricio Pochettino, ya tabbatar da cewar Harry Kane ya yi rauni, amma bai bayyana kwana nawa zai yi jinya ba.
Kane mai shekara 23, ya yi rauni ne a karawar da Tottenham ta ci Sunderland 1-0 a White Hart Lane a gasar Premier a ranar Lahadi.
Dan kwallon tawagar Ingila, ya yi wa Tottenham wasanni Premier 71 a jere, kuma shi ne wanda ya fi ci wa kungiyar kwallaye a kakar wasanni biyu baya.
Harry Kane ne ya lashe kyautar dan wasan da ya fi zura kwallo a raga a Premier da aka kammala, inda ya ci 25.