Wanne darasi Nigeria ta dauka bayan Paralympic

Nigeria
Bayanan hoto,

Are Feyisetan daga bangaren dama shi ne ya jagoranci tawagar daga nauyi ta Nigeria a gasar Paralympic da aka yi a Brazil

A ranar Lahadi aka kammala wasannin Paralympic na nakasassu a birnin Rio na Brazil, inda Nigeria ta yi ta 17 a yawan lashe lambobin yabo a wasannin.

Tawagar ta Nigeria ta ci lambobin yabo 12, zinare takwas da azurfa biyu da tagulla biyu, ita ce ta jagoranci Afirka a yawan lashe lambobin yabo.

Tawagar ta nakasassu ta dara ta masu lafiya kokari, wadanda makonnin baya da suka wuce suka ci tagulla daya a wasan kwallon kafa, suka kare a mataki na 78 a gasar.

Nakasassun na Nigeria wadan da suka fara wakiltar kasar a gasar Paralympic a shekarar 1992 a Barcelona, sun ci gaba da taka rawa wajen wakiltarta.

A gasar Olympics da aka yi a Landan a 2012 ba a daga tutar Nigeria ba, domin ba ta ci lambar yabo ko daya ba.

Amma 'yan wasan nakasassu suka ci lambobin yabo 13 a wasannin Paralympic da aka yi a Landan din.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Josephine Orji daya daga cikin wadan da suka ci wa Nigeria zinare a Rio

Nasarar da suka samu abin a jinjina musu ce idan aka yi la'akari da mawuyancin halin da kyama da duk wani nakasasshe a Nigeria ke fuskanta.

A wasannin Paralympic na bana da aka yi a Brazil, Nigeria ta ciri tuta a wasan daga nauyi, inda ta ci zinare shida da azurafa biyu da tagulla daya.

A fagen daga nauyin a wasannin Paralympic ba za a manta da Are Feyisetan wanda ya jagoranci tawagar Nigeria lashe lambobin yabo a Brazil ba.

Zakaran daga nauyi a baya can, Feyiseten, ya kafa kungiyar kwallon kafa ta nakasassu a shekarar 2002.

Feyiseten ya ce wasan daga nauyi ya wuce wasa, domin wadanda yake horarwa na fada masa cewar dama ce da suke manta damuwar da ke damunsu da talaucin da suke ciki.

Kociyan ya kara da cewar mutane sun dauka cewar dole ne nakasasshe ya yi bara, amma sun kauda wannan tunanin.

Ya kuma ce mutane na mantawa da cewar wasu daga cikinsu mutane ne masu lafiya kamar kowa, sukan ci karo da hadarurrukan da ke kai wa a yanke musu kafafu, daga nan ne suka shiga wasan daga nauyi.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Roland Ezuruike shi ma ya ci wa Nigeria zinare a Rio

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

'Yan wasan na Nigeria sun taka rawa a wasannin Paralympic duk da rashin samun isasshen horo da karancin kayayyakin wasa da rashin tallafi.

Kayayyakin da nakasassun ke yin atisayen, an samar da su ne tun a shekarar 1990, kuma har yanzu da su suke amfani.

Suna kuma yin atisaye a karyayyun benci a daki mai duhu a katafaren filin wasa da ke Legas, ga matalar cinkoson hanya, mai kafa ma yana kokawa balle nakasasshe wajen zuwa wajen atisaye.

'Yan wasan ba sa samun kamfanoni ko jama'a da suke daukar nauyin wasanninsu, kowa ya gwammace ya dauki nauyin kwallon kafa.

Kwallon kafa ne wasan da ke kan gaba a Nigeria da 'yan kasar ke sha'awa, kuma shi ne ke hada kan 'yan kasar ba tare da kabilanci ko addini ko siyasa ba.

Babu yadda za ka hada tsakanin kwallon kafar kasar da 'yan wasan tawagar Nigeria da suke wakiltarta a Paralympic.

Duk da miliyoyin kudaden da ake kashewa 'yan kwallon kafar Nigeria a kowacce shekara, sun kasa samun shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka sau biyu a jere, duk da dunbin yawan al'umma da ke kasar.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

Lauritta Onye ta ci wa Nigeria zinare a wasan jifan dalma

Idan ka auna nasarar da tawagar Nigeria ta kai zuwa mataki na biyu a gasar kofin duniya da aka yi a 2014 da kuma lashe kofin Afirka a 2013, tun daga nan ne ta yi ta yin baya a tamaula.

Nigeria ta lashe tagulla a wasan kwallon kafa a gasar Olympic da aka yi a Brazil, koda yake wasannin na matasa ne 'yan kasa da shekara 23, amma su ne suke buga wa Super Eagles wasanni a gaba.

Wane darasi Nigeria ta samu dangane da kwallon kafa da ta bai wa fifiko.

Na farko da'a:

'Yan wasan daga nauyi na Nigeria kan bar gida zuwa wajen atisaye tun daga karfe biyar, domin suna fara wasanni da karfe shida a duk ranar Litinin da Talata da Juma'a.

Duk da rashin daukar nauyin wasannin na su ba su taba kauracewa gasa ba, ko kuma fadawa duniya cewar ba a biya su albashi ba.

Juriya:

Feyiseten ya fara horar da tawagar daga nauyi ta Nigeria tun a shekarar 2006, kuma har yanzu yana jan ragama, an kuma yi masa tayin aiki a wurare da dama, amma ya ki amincewa.

A tsawon lokacin da ya yi yana horar da 'yan wasan daga nauyi nakasassu na Nigeria, tawagwar kwallon kafa kasar ta sauya masu horar da ita sau 11.

Adalci:

Idan aka zo gasar kwallon kafa, mahukunta kan tursasa a saka wasu 'yan wasan ko ana so ko ba a so, amma hakan ba zai yi wu ba a wasannin daga nauyi.

'Yan jaridu da kafafen sada zumunta kan dauke hankulan 'yan wasan kwallon kafa a lokacin tunkarar wasanni, yayin da 'yan wasan daga nauyi da ba kowa ne ya sansu ba kan mayar da hankali wajen gasar da ke gabansu.