Dan Kanawa ya buge Inda a damben gasar mota

Gargajiya
Bayanan hoto,

Motar da za a bai wa wanda ya zama zakara a gasar damben gargajiya a Kano

Ibrahim Dan Kanawa ya buge Inda a damben gargajiya na gasar da za a lashe mota a karawar da suka yi a ranar Talata a filin wasa na Ado Bayero Square da ke jihar Kano.

Sauran wasannin da aka yi Sojan Dogon Jango ya yi nasara a kan Shagon Bahagon Bala, Bahagon Sama'ila ya buge Nura Dan Karami.

A wasan karshe a ranar ta Talata, Kurarin Kwarkwada ya fitar da Shagon Kara Mutsa daga gasar.

Za a ci gaba da wasanni a ranar Laraba a filin wasa na Ado Bayero Square da ke jihar Kano.