Arsenal ta ci Nottingham Forest 4-0

Asalin hoton, Getty Images
David Ospina ne ya tsare ragar Arsenal a wasan da ta yi 1-1 da PSG a gasar zakarun Turai
Nottingham Forest ta yi rashin nasara da ci 4-0 a hannun Arsenal a gasar Capital One Cup wasan zagaye na uku da suka yi a ranar Talata.
Granit Xhaka ne ya fara cin kwallo kuma da haka aka je hutun rabin lokaci.
Bayan da aka dawo ne Pérez Martínez ya ci guda biyu kuma daya a bugun fenariti sannan Oxlade-Chamberlain ya ci ta hudu.
Sauran sakamakon wasannin da aka yi:
- Derby County 0 vs 3 Liverpool
- Newcastle United 2 vs 0 Wolverhampton
- Brighton & Hove Albion 1 vs 2 Reading
- Leeds United 1 vs 0 Blackburn Rovers
- Nottingham Forest 0 vs 4 Arsenal
- Everton 0 vs 2 Norwich City