Wales ta ci riba bayan gasar kofin nahiyar Turai

Asalin hoton, Huw Evans picture agency
Kokarin da Wales ta yi a gasar nahiyar Turai ya sa kasar ta shiga cikin goman farko a jadawalin kasashen da suka fi iya taka leda a duniya da Fifa ta fitar.
Hukumar kwallon kafa ta Wales ta ci ribar fam miliyan uku, bayan da tawagar kasar ta kai wasan daf da karshe a kofin nahiyar Turai.
Babban jami'in hukumar, Jonathan Ford ya ce za su bunkasa wasannin kwallon kafa a Wales da samar da kayayyakin wasanni.
Sai dai kuma Ford ya ce kasar tana koma baya a fagen tamaular mata a tsawon lokaci, inda Ingila da Jamus suka yi mata fintinkau.
Ford ya ce za su mai da hankali wajen bunkasa wasannin kwallon kafar mata domin Wales ta yi fice nan gaba a duniya.