Ba za a dambata tsakanin Mayweather da McGregor ba

Dambatawa

Asalin hoton, Mayweather Mcgregor

Bayanan hoto,

Mayweather ya ce daf ya rage ya sake dawowa ruwa domin ya dambata da McGregor

Tsohon zakaran damben boksin na duniya, Floyd Mayweather, wanda ya yi ritaya ya ce ba zai dambata da Conor McGregor.

Tun farko Mayweather dan Amurka zakaran damben boksin karo biyar ya bukaci a biya shi dala miliyan 100 , domin ya kara da McGregor mai shekara 28.

Mayweather ya ce an karramashi da har aka bukaci ya dambata, amma ya riga ya yi ritaya ba zai dawo wasan ba.

McGregor ya fada a baya cewar ya so ya dambata da Mayweather duk da cewar ya yi ritaya daga damben boksin..