Valencia ta kori kociyanta Ayestaran

Pako Ayestaran

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Pako Ayestaran ya yi wa Rafael Benited kociyan Newcastle na yanzu mataimaki

Valencia ta raba gari da kociyanta Pako Ayestaran, bayan da kungiyar ta yi rashin nasara a wasanni hudu a jere a gasar La Liga da ta buga.

Ayestaran mai shekara 53, ya maye gurbin Gary Neville a watan Maris din bara,

Kociyan ya yi rashin nasara a wasanni takwas daga 12 da ya jagoranci kungiyar, kuma Valencia ce ta karshe a kan teburin La Liga na bana.

Wasan da ya jagoranci Valencia na karshe shi ne wanda ta yi rashin nasara da ci 2-1 a hannun Athletic Bilbao a ranar Lahadi.

Valencia ta nada Salvador Gonzalez Marco, wanda aka fi sani da suna 'Voro', a matasyin kociyan rikon kwarya, karo na hudu kenan yana aikin..

Ayestaran ya yi wa kociyan Newcastle United Rafael Benitez mataimaki a kungiyoyi biyar ciki har da Valencia da kuma Liverpool.