Antalyaspor ta dakatar da Samuel Eto'o

Kociya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Eto'o ya ci kwallaye 21 a wasanni 34 da ya buga wa Antalyaspor ya kuma rike matsayin kociyan rikon kwarya na kungiyar

Antalyaspor ta dakatar da Samuel Eto'o daga buga mata wasanni, saboda kalaman da ya yi a shafinsa na sada zumunta.

Tsohon kyaftin din Kamaru, mai shekara 35, ya rubuta a shafinsa na Instagram cewar "Wasu mutanen ba sa martabani, saboda ni bakar fata ne".

Daga baya Eto'o ya mayar da martani kan zargin da ake yi masa cewar yana magana ne kan shugaban kungiyar Safak Ozturk.

Ozturk ya zargi Eto'o da laifin kasa taka rawar gani a farkon wasannin kakar bana.

Antalyaspor ta fitar da sanarwar cewar Eto'o zai dinga yin atisaye da za a tsara masa na da ban, har zuwa lokacin da mahukuntan kungiyar za su yi taro kan dan kwallon.