Blackburn Rovers ta dauki Wes Brown

Manchester

Asalin hoton, Rex Features

Bayanan hoto,

Brown tsohon dan wasan kungiyar Manchester United ne

Blackburn Rovers ta dauki Wes Brown domin ya buga mata tamaula zuwa karshen kakar wasanni ta bana.

Yarjejeniyar Brown mai shekara 36 ce ta kare da Sunderland wadda ya buga wa tamaula tsawon shekara biyar.

Cikin yarjejeniyar da dan wasan ya saka hannu zai taimakawa kociyan matasan Blackburn masu shekara 23.

Rovers tana mataki na biyun karshe a kan teburin Championship da maki biyar a wasanni takwas da ta buga a gasar.