Za mu yi nazari a kan burinmu — Ingila

Ingila ta kasa taka rawar gani a gasar cin kofin nahiyar Turai da aka yi a Faransa
Shugaban hukumar kwallon kafa ta Ingila, Greg Clarke, ya ce za su sake yin nazari a kan burin da suke son ganin tawagar kwallon kafar yankin ta cimma.
Clarke ya fadi hakan ne a bikin kaddamar da shirin karbar bakuncin Gasar cin Kofin Nahiyar Turai ta shekarar 2020 a Landan.
Ya kara da cewa za su dora tawagar kwallon kafar ta Ingila a kan turba, ta yadda za ta dinga taka rawar gani a gasar wasanni.
Iceland ta kunyata Ingila a wasan zagaye na biyu a Gasar cin Kofin Nahiyar Turai da aka yi a Faransa.
A baya, hukumar kwallon kafa ta Ingila a karkashin jagorancin Greg Dyke ta sha alwashin lashe Gasar Kofin Nahiyar Turai ta 2020 da kuma Kofin Duniya na 2022.