Bahagon Sani ya kai zagayen gaba a damben mota

Gargajiya
Bayanan hoto,

Bahagon Sanin Kurna ya kai zagayen gaba a gasar damben mota ta Kano

Bahagon Sanin Kurna ya kai wasan zagayen gaba a gasar damben gargajiya da za a lashe mota, wadda ake yin gumurzu a filin wasa na Ado Bayero Square da ke jihar Kano.

Bahagon Sanin Kurnan ya kai wasan zagayen gaban ne bayan da ya doke Garkuwan Shagon Alabo.

Shi ma Shagon Buhari ya samu nasara ne a kan Shagon a Bata Mai, yayin da Ali Kanin Bello ya buge Bahagon Dogon Auta.

A karawar karshe da aka yi a yammacin Laraba, Shagon Sama'ila ya yi nasara a kan Shagon Alhazai.

Za a ci gaba da wasanni a ranar Alhamis:

  • Shagon Mada da Garkuwan Shagon 'Yan Sanda
  • Shagon Aleka da Bahagon Na Bacirawa
  • Garkuwan Mai Caji da Bahagon Audu Argungu
  • Ebola da Bahagon Balan Gada