An dakatar da masu horar da Mongolia kokawa

Kokawa

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Hukumar ta dakatar da masu horarwa daga shiga sabgogin kokawa har tsawon shekara uku.

Hukumar wasan kokawa ta duniya ta dakatar da masu horar da Mongolia wasan su biyu, bayan da suka cire kayansu da nufin yin bore ga hukuncin da aka yanke musu a Gasar Olympic a Rio.

Tserenbaatar Tsogbayar da kuma Byambarinchen Bayaraa sun yi boren ne kan hukuncin da alkalan wasa suka yanke a kan Ganzorigiin Mandakhnaran a wasan neman tagulla.

Hukumar ta dakatar da masu horarwa daga shiga sabgogin kokawa har tsawon shekara uku.

Haka kuma hukumar ta ci tarar Mongolia kudi sama da fam 39,000.