Villareal ta taka wa Real Madrid burki

Madrid

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Real Madrid tana mataki na daya a kan teburin La Liga da maki 13

Real Madrid da Villareal sun tashi wasa kunnen doki 1-1 a gasar La Liga mako na biyar da suka kara a ranar Laraba.

Madrid ce ta fara cin kwallo ta hannun Sergio Ramos, yayin da Villareal ta farke ta hannun Bruno Soriano a bugun fenariti.

Da wannan sakamakon Villareal ta taka wa Madrid yawan lashe wasannin La Liga da ta yi 16 a jere.

Madrid din ta kafa tarihin lashe wasannin La Liga 16 a jere a ranar Lahadi, bayan da ta ci Espanyol 2-0, kuma ta yi kan-kan-kan da Barcelona wadda ta fara kafa tarihin a 2010/11.