Man United ta kai zagayen gaba a Capital Cup

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United ta kai wasan zagaye na biyu a gasar ta Capital One Cup
Manchester United ta doke Northampton Town da ci 3-1 a gasar Capital One Cup wasan zagaye na uku da suka kara a ranar Laraba.
Michael Carrick ne ya fara ci wa United kwallo, Northampton Town ta farke ta hannun Revell daf da za a je hutu a bugun fenariti.
Bayan da aka dawo ne daga hutu United ta kara cin kwallaye biyu ta hannun Ander Herrera da Marcus Rashford.
Sakamakon wasu wasannin da aka buga:
- Fulham 1 Bristol City 2
- QPR 1 Sunderland 2
- Southampton 2 Crystal Palace 0
- Swansea 1 Man City 2
- West Ham 1 Accrington 0