Man Utd za ta kara da Man City a gasar kofin EFL

Jose Mourinho da Pep Guardiola

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kocin City Pep Guardiola ne ya yi nasara a karawar farko a Old Trafford

Manchester United za ta karbi bakuncin Manchester City a wasan zagaye na hudu na gasar cin kofin EFL a filin wasa na Old Trafford.

United ta samu nasara 3-1 a kan Northampton a ranar Laraba, yayin da City ta doke Swansea da ci 2-1 har gida.

Wannan ne karo na biyu da kungiyoyin za su kara a bana bayan haduwar da suka yi a ranar 10 Satumba.

A sauran wasannin kuma, West Ham za ta karbi bakuncin Chelsea, yayin da Tottenham za ta yi tattaki zuwa Liverpool.

Za a buga wasannin ne a makon da zai fara daga 24 ga watan Oktoba.

Ga wasannin da za a fafata:

West Ham da Chelsea

Manchester United da Manchester City

Arsenal da Reading

Liverpool da Tottenham

Bristol City da Hull

Leeds da Norwich

Newcastle da Preston

Southampton da Sunderland