Dangote zai sayi Arsenal nan da shekara hudu

Arsenal

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ba wannan bane karon farko da Dangote ke sanar da aniyarsa ta son sayen kungiyar kwallon kafa ta Arsenal

Attajirin dan kasuwar da ya fi kowa arziki a Afirka, Aliko Dangote na shirin sayen kungiyar kwallon kafa ta Arsenal nan da shekara hudu.

Dangote, dan Najeriyar da ya mallaki kadarar da ta kai sama da dala biliyan 10 in ji mujallar Bloomberg, ya taba sanar da burinsa na sayen Arsenal a bara.

Attajirin ya ce yana jiran arzikinsa ya kara bunkasa da jarin da ya saka a harkar gas da matatar mai kafin ya taya kungiyar ta Arsenal.

Ya kuma ce zai sayi Arsenal ne domin yin kasuwanci kamar yadda ya saba, ya gudanar da kasuwanci da dama ya kuma samu nasara, inda yake fatan daga darajar kungiyar.

Dangote, wanda mai goyon bayan Arsenal ne, ya yi asarar sama da dala biliyan hudu a bana, sakamakon karyewar darajar kudin Najeriya.

Arsenal ta lashe kofin Premier ta Ingilasau 13, kuma tana cikin kungiyoyin da suke taka rawar gani a Turai, sai dai rabon da ta dauki kofin Premier tun a shekarar 2004.

Sau da dama Dangote ya sanar da cewa zai sayi Arsenal, sai dai kuma abin tambaya shi ne, me zai hana ya bunkasa wasannin Najeriya da Afirka?

Shin ina aka kwana kan maganar da ya yi cewar zai taimakawa tawagar kwallon kafar Najeriya?