Messi zai yi jinyar mako uku

Asalin hoton, Getty Images
Barcelona tana mataki na uku a kan teburin La Liga
Dan kwallon Barcelona, Lionel Messi, zai yi jinyar mako uku, bayan da ya yi rauni a karawar da kungiyar ta tashi 1-1 da Atletico Madrid a Camp Nou.
Kungiyoyin biyu sun kara ne a wasan mako na biyar a gasar La Liga a ranar Laraba.
Messi ya yi rauni ne bayan da aka koma hutun rabin lokaci, inda Arda Turan ya canje shi a karawar.
Messi ba zai buga wa Barcelona wasanni uku ba ke nan -- ciki har da karawar da za ta yi da Sporting Gijón da Celta Vigo da kuma wanda za ta yi da Borussia Mönchengladbach a gasar kofin zakarun Turai.
Barcelona tana mataki na uku a kan teburin La Liga da maki 10, inda Real Madrid ke matsayi na daya da maki 13, Sevilla ce ta biyu da maki 11.