Za a raba jadawalin kwallon rairayi na Afirka

Asalin hoton, The NFF
Kasashe biyu ne za su wakilci Afirka a gasar kwallon rairayi da za a yi a shekarar 2017 a Bahamas
Hukumar kwallon kafa ta Afirka, Caf, za ta raba jadawalin kwallon rairaiyi a gasar kofin nahiyar Afirka a ranar Asabar a Masar.
Kungiyoyin da za su fafata a gasar sun hada da Nigeria -- mai masaukin baki -- da Masar da Ghana da Libya da Madagascar da Morocco da kuma Senegal.
Za a fara gasar kwallon rairayi ta cin kofin nahiyar Afirka daga ranar 13 ga zuwa 18 ga watan Disambar 2016 a Legas.
Kungiyoyi biyun da suka kai wasan karshe za su wakilci Afirka a gasar kwallon rairayi ta duniya da za a yi a Bahamas a 2017.