Busquets zai ci gaba da taka-leda a Barcelona

Barcelona

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sergio Busquets ya koma Barcelona da murza-leda a kakar wasan 2008/09 karkashin jagorancin Pep Guardiola

Sergio Busquets ya sabunta yarjejeniyar ci gaba da buga wa Barcelona tamaula zuwa shekarar 2021 a ranar Alamis.

Barcelona da dan kwallon sun kuma cimma yarjejeniyar cewar za a iya tsawaita zamansa a Camp Nou a 2023 bisa yawan wasannin da ya yi wa kungiyar.

Busquets ya yi Barcelona wasanni 390 ya kuma ci mata kwallaye 12, tun komawarsa kungiyar da taka-leda a 2008/09 karkashin jagorancin Pep Guardiola.

Dan wasan ya lashe kofin zakarun Turai uku a Barcelona da na La Liga shida da na Spanish Cup hudu da kofin duniya na zakarun nahiyoyi da European cup uku da na Spanish Super Cup biyar.