Rose ya sabunta kwantiragi a Tottenham

Rose zai ci gaba da buga wa Tottenham tamaula har zuwa shekarar 2021
Mai tsaron baya Danny Rose, ya sabunta yarjejeniyar ci gaba da buga wa Tottenham kwallo har zuwa shekarar 2021.
Rose mai shekara 26, ya yi wa Tottenham wasanni 126, inda ya ci mata kwallaye tara, tun lokacin da ya koma can da murza-leda a Yulin 2007 daga Leeds United.
Dan kwallon ya buga wa tawagar kwallon kafa ta Ingila wasanni takwas, inda ya fara wasan farko a karawar da Ingila ta ci Jamus 3-2 a Berlin a watan Maris.
Rose ya buga wa Ingila wasanni uku daga cikin hudun da ta fafata a gasar cin kofin nahiyar Turai da aka yi a Faransa.