Birtaniya za ta kara da Canada a Davis Cup

Kwallo

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Murray da Raonic sun kara a wasan karshe a gasar kwallon tennis ta Wimledon, kuma Murray ne ya yi nasara

Birtaniya za ta fafata da Canada a wasan zagayen farko a gasar kwallon tennis ta Dais Cup a cikin watan Fabrairu.

A makon da ya wuce ne Argentina ta ci Birtaniya 3-2 a wasan daf da karshe a Davis Cup a karawar da suka yi a Glasgow.

Gumurzun da za a yi tsakanin Andy Murray dan wasan Birtaniya da Milos Raonic na Canada, za su yi ne tsakanin 3 zuwa 5 ga watan Fabrairu.

Murray ya doke Raonic a wasan karshe a gasar kwallon tennis ta Wimledon, inda ya samu damar lashe babbar gasar tennis karo na uku.