Rome za ta janye daga zawarcin Olympic

Olympic

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Haka ma biranen Boston da Hamburg sun janye daga neman izinin shirya gasar ta Olympic ta 2024

Birnin Rome na shirin janyewa daga zawarcin karbar bakuncin Gasar Olympic ta 2024, inda shugabar birnin ta ce bai dace su shirya wasannin ba.

Jawabin da Virginia Raggi ta yi, inda ta sanar da matakin, ya karya gwiwar kwamitin karbar bakuncin gasar na birnin wanda suka so sauya mata ra'ayi.

Birnin Rome ya taba karbar bakuncin Olympic a 1960, ya kuma taba janyewa daga zawarcin gasar 2020 bisa dalilin karyewar tattalin arziki.

Haka ma biranen Boston da Hamburg sun janye daga neman izinin shirya gasar ta Olympic ta 2024.

Sai dai kuma biranen Paris da Los Angeles da kuma Budapest suna ci gaba da zawarcin wasannin Olympic din, wanda za a bayyana masu son karbar bukuncin gasar a ranar 7 ga watan Oktoba.