An fitar da Shagon Mada a damben Mota

Dambata
Bayanan hoto,

Shagon Mada bai halarci gasar da ya kamata ya dambata a ranar Alhamis ba

Shagon 'Yan Sanda ya kai zagayen gaba a gasar damben gargajiya da za a lashe mota, wadda ake yi a gidan wasanni na Ado Bayero Square da ke jihar Kano.

Shagon 'Yan Sandan ya kai zagayen gaba ne, bayan da Shagon Mada bai halarci wasan da aka tsara tun farko za su dambata ba.

Shi kuwa Bahagon Na Bacirawa ya buge Shagon Aleka, yayin da Garkuwan Mai Caji ya kai zagayen gaba bayan da ya samu nasara a kan Shagon Audu Argungu.

Ebola da Bahagon Balan gada an yi waje da su daga gasar, bayan da basu halarci wasannin ba.

Za a ci gaba da gasar a ranar Juma'a a filin wasa na Ado Bayero da ke jihar Kano.