Aleka da Dogon Bunza sun yi canjaras

Dambe
Bayanan hoto,

Aleka da Dogon Bunza sun dade suna dambatawa a tsakaninsu

Aleka da Dogon Bunza sun tashi dambe canjaras a karawar da suka yi a gidan damben Ali Zuma da ke Dei-Dei a ranar Alhamis.

Aleka dan wasan Kudu da Dogon Bunza daga Arewa sun yi turmi uku suna dambatawa, amma babu wanda ya je kasa a tsakaninsu.

Sa zare ma da aka yi tsakanin Bahagon Mai Maciji da Nuran Dogon Sani turmi uku suka yi babu kisa, alkalin wasa Tirabula ya raba su.

Sai dai kuma Shagon Mai Maciji ya doke Bahagon Soja a turmin farko, yayin da Shagon Fijo ya buge Shagon Bahagon Sisco a turmin farko.

Za a ci gaba da wasanni a ranar Juma'a da yammaci.