Ryan Giggs zai so ya zama kocin Swansea

Ryan Giggs

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ryan Giggs ya shafe shekara 29 a Manchester United

Ryan Giggs zai so ya karbi jagorancin kulob din Swasea idan aka sallami kocin kulob din na yanzu Francesco Guidolin.

Giggs, mai shekaru 42, ya bar matsayinsa na mataimakin kocin Manchester United a farkon watan Yuli - abin da ya kawo karshen shekara 29 da ya shafe a kungiyar.

Swansea ta samu maki hudu ne kawai a wasanni biyar din da ta buga, kuma rahotanni sun ce kungiyar na son sauya mai horas da 'yan wasanta.

Sai dai ko da za a nada sabon kocin, ba lallai ba ne ace Giggs ne kawai za a yi wa tayin aikin.

Tun bayan da ya bar Old Trafford a watan Nuwamba, dan kasar ta Wales ya mayar da hankali ne kan harkokin kasuwancinsa da ya dade yana yi.

Da kuma kula da kulob din Salford City da ya mallaka tare da Paul Scholes, Nicky Butt, Gary Neville da and Phil Neville.

Giggs ya kuma kammala dukkan karatun kocin da ya kamata ya yi, kuma bai boye aniyarsa ta koyar da tamola ba.