Ba a san ranar da Kompany zai dawo tamaula ba

Kompany

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Manchester City ce ta daya a kan teburin Premier

Manchester City ba ta san ranar da kyaftin dinta Vincent Kompany zai dawo taka-leda ba, bayan da yake yin jinya a yanzu haka.

Mai tsaron baya, mai shekara 30, ya yi rauni a wasan da City ta doke Swansea 2-1 a gasar Capital One Cup a ranar Laraba.

Wasan kuma shi ne na farko da ya buga wa City a kakar wasan bana, tun wanda ya murza mata leda a ranar 4 ga watan Mayu.

Manchester City ta ci gaba da zama a Kudancin Wales domin ta sake karawa da Swansea a gasar Premier a ranar Asabar.