Man United za ta karbi bakuncin Leicester

Premier

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

United ce ta ci Leicester a Community Shield da suka kara a bana

Leicester City za ta ziyarci Manchester United a gasar Premier wasan mako na shida da za su kara a Old Trafford a ranar Asabar.

Kungiyoyin biyu sun kara a Community Shield a ranar 7 da watan Agusta 2016, inda United ta ci Leicester 2-1 a Wembley.

A gasar Premier da aka yi ta bara a wasanni biyu da kungiyoyin biyu suka fafata sun tashi kunnen doki 1-1 ne.

Kociyan Leicester, Claudio Ranieri, bai yi rashin nasara a hannun Jose Mourinho a karawa hudu baya da suka yi ba, inda ya ci wasanni biyu suka yi canjaras a fafatawa biyu.

United tana mataki na bakwai a kan teburin Premier da maki tara, yayin da Leicester City mai rike da kofin ke matsayi na 11 da maki bakwai