Man City ta kankane teburin Premier

Har yanzu Manchester City ce take kan gaba a teburin gasar Premier
Bayanan hoto,

Manchester City ta cinye wasanninta na farko guda shida

Kulob din Manchester City wanda shi ne jagaba a teburin gasar Premier, ta kara samun nasara cigaba da yin jagora a gasar, bayan samun nasara a kan Swansea.

Dan wasan Man City, Sergio Aguero ne dai ya fara jefa kwallo a ragar Swansea, kafin Fernando Llorente ya ci wa Swansea a tazarar minti hudu.

Agueron dai ya kara kwallo ta biyu a dukan fanaret sakamakon gular da Mike van der Hoorn ya yi wa Kevin de Bruyne.

Raheem Sterling ne kuma ya ci wa Man City din kwallo ta uku.

Yanzu haka, Pep Guardiola koci na biyu da ya iya cin wasanninsa guda shida na farkon gasar Premier.

Carlo Ancelotti ne dai mutum na farko da ya yi hakan lokacin da ya kai Chelsea ga daukar kofi, a 2009-10.