Arsenal ta casa Chelsea 3-0

Lokacin da Ozil ke kwarara kwallo a ragar Chelsea kenan

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Sau biyu kenan Mesut Ozil na ci wa Arsenal kwallo a bana

Arsenl ta samu nasararta ta hudu a jere a gasar Premier bayan da ta casa Chelsea da ci 3-0.

Alexis Sanchez ne ya fara daga ragar Chelsea a minti 11 da wasa, kafin kuma Theo Walcott ya kara ta biyu bayan minti uku.

Saura minti biyar a tafi hutun rabin lokaci sai Mesut Ozil ya ci ta uku bayan da suka yi wani ba-ni-in-ba-ka da Sanchez.

Wannan shi ne rashin nasara da Chelsea ta yi a karo na biyu a jere a gasar ta bana, lamarin da ya sa ta koma ta takwas a tebur da maki goma, yayin da Arsenal ta daga zuwa matsayi na uku da maki 13.

Bayan wasan na mako na shida Man City ta ci gaba da rike matsayi na daya da maki 18, sakamakon kashin da ta je ta ba wa Swansea a gida 3-1.

Tottenham wadda ta bi Middlesbrough gida ta ci ta 2-1 ta zama ta biyu a teburin na Premier da maki 14.

Liverpool ma ta matsa gaba zuwa matsayi na hudu da maki 13 da bambabncin kwallo daya tsakaninta da Arsenal, bayan ta lallasa Hull City 5-1.

Bayanan da ya kamata ka sani game da wasan Arsenal:

Kwallon da Ozil ya ci ita ce ta biyu da ya ci wa Arsenal a bana.

Wannan shi ne rashin nasara mafi girma da Antonio Conte ya gamu da shi a wata gasar Lig tun watan Oktoba na 2010 lokacin da Empoli ta ci kungiyarsa Siena 3-0.

Wannan shi ne karon farko da Arsene Wenger ya ci Chelsea a gasar Premier tun watan Oktoba na 2011( ya yi canjaras sau uku kuma ya yi rashin nasara sau 6).

Wasannin gaba na Arsenal da Chelsea:

A ranar Laraba Arsenal za ta yi wasan Kofin Zakarun Turai a gida da FC Basel ta Switzerland, yayin da Chelsea za ta yi wasanta na gaba na Premier da Hull City ranar Asabar mai zuwa.